UEFA: Wainar da aka toya

  • CSKA ta ci kasuwar Manchester City
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Doumbia ne ya ci kwallaye biyu

Bayan nasarar CSKA Moscow a kan Manchester City da ci biyu da daya, a yanzu hankali ya karkata a kan salon wasan Manuel Pellegrini a gasar zakarun Turai.

Dan kwallon Ivory Coast, Seydou Doumbia ne ya zura kwallaye biyu a wasan.

Sakamakon ya bar City can a matsayin ta karshe a kan teburi a yayinda Bayern ke farko, CSKA da Roma suke matakin na biyu da na uku.

  • Mako mara dadi ga kungiyoyin gasar Premier ta Ingila
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal ta sha mamaki a Emirates

Sakamakon wasan City shi ne mafi muni idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin gasar Premier ta Ingila a wannan makon, amma kuma za a iya tsokaci a kan Arsenal ko Chelsea ko Liverpool.

Arsenal ta zura kwallaye uku a ragar Anderlect a Emirates amma kuma sai aka farke duka kwallayen aka tashi uku da uku. Ita ma Chelsea ta tashi kunen doki daya da daya tsakaninta da Maribor ta Slovenia.

A yayinda Real Madrid ta casa Liverpool da ci daya mai ban haushi.

  • Taka rawa a gida daban ne da gasar Turai
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galatasaray ta kwashi kashinta a hannu

Borussia Dortmund ta tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar Zakarun Turai amma a yanzu ita ce ta kusa da karshe a kan teburin gasar Bundesliga bayan rashin nasara a wasanni biyar a jere.

Ita ma Galatasaray ta sha kashi da ci hudu da nema a hannun Borussia amma kuma ita ce ta farko a kan teburin gasar kwallon Turkiya.

  • Shakhtar ta haskaka duk da rashin matsuguni
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shakhtar na tsaka mai wuya a Ukraine

Shakhtar Donetsk na Ukraine a yanzu ta na buga gasar zakarun Turai ne a birnin Lviv da ke da tazarar mil 640 daga filinta na asali wanda aka jefawa bam sau biyu.

Amma duk da haka ta na kan hanyar tsallakewa zuwa zagaye na gaba musamman bayan lallasa BATE Borisov da ci 7 da 0 da kuma 5 da 0 a wasanni biyu.

Dan Brazil, Luiz Adriano ya zura kwallaye takwas a wasannin.

  • Messi da Ronaldo suna hammaya
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya shiga gaban Ronaldo

Ana kallonsu a matsayin 'yan wasan da suka fi kowanne haskaka a wannan zamanin.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a yanzu suna kokarin kafa tarihi kan zura kwallo a gasar zakarun Turai.

Messi ne kan gaba saboda kwallaye biyun da ya zura a wasan da Bercelona ta doke Ajax daci biyu da nema inda ya kamo Raul wajen zura kwalleyn 71, a yayinda shi kuma Ronaldo yake da kwallaye 70.

Ronaldo ya zura kwallaye 12 a wasanni 12 a jere kafin ya kasa cimma burinsa a wasansu da Liverpool a ranar Talata.