Chelsea ta doke Liverpool 2-1 har gida

Liverpool Chelsea Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu Chelsea ta ci gaba da rike matsayinta na daya a teburin Premier

Chelsea ta ci gaba da rike matsayinta na daya a teburin Premier, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka kara a Anfield ranar Asabar.

Emre Can ne ya fara zura kwallo a raga, kafin daga baya Garry Cahill ya farke kwallon da aka yi takaddamar shiga raga, inda alkalin wasa ya tabbatar da shigarta ta na'ura mai auna idan kwallon ta haura layin raga.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Chelsea ta kara kwallo ta biyu ta hannun Diego Costa, kuma kwallo na 10 da ya zura a gasar Premier Bana.

Chelsea ta ci gaba da zama a matsayi na daya a teburin Premier da maki 29, kuma har yanzu babu wata kungiya da ta doke ta bayan buga wasanni 11.

Liverpool za ta ziyarci kulob din Crystal Palace a wasan mako na 12, yayin da Chelsea za ta karbi bakuncin West Brom a Stamford Bridge.