Morocco ta kasa cika wa'adin CAF

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hassan Shehata ke nan a lokacin hada jadawalin yadda kasashe za su hadu a gasar ta Morocco

Morocco ta gaza wajen cimma wa'adin da aka ba ta, na tabbatar da ko za ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta nahiyar Afurka a shekara 2015 ko ba za ta iya ba.

Tun da fari kasar ta bukaci a dage wasan tare da kara shekara guda, saboda tsoron ka da 'yan kallo da za su zo daga kasashen waje su yada cutar Ebola.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Afurka CAF ta ki amincewa da hakan, tare da zargin Morocco da zuzuta fargabar yada cutar ta Ebola.

Wakilin BBC a harkar wasanni ya ce babu wata kasa da za ta maye gurbin Morocco ganin cewar sauran kasashe ba su ce uffan ba.

Tuni Afurka ta kudu da ta karbi bakuncin wasan shekarar da ta gabata, ta ce ba za ta sake karbar bakuncin wasan ba a shekara mai zuwa.

Karin bayani