Mun dora wa Rooney nauyi mai yawa - Hodgson

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun da ya karbi kyaftin din Ingila sun lashe wasanninsu uku

Kocin tawagar kwallon kafar Ingila Roy Hodgson ya damu cewar nada Rooney a kyaftin, ya karamasa nauyi kuma yana tsoron kada ya saka masa rashin natsuwa a wasa.

Rooney dan kwallon Manchester United mai shekaru 29, an ba shi kyaftin din Ingila a watan Agusta, kuma zai buga wa kasar wasa na 100 a karawar da za su yi da Slovenia ranar 15 ga watan Nuwamba a Wembley.

Tun lokacin da aka bai wa Rooney kyaftin din tawagar kwallon kafar Ingila, sun lashe wasanni uku a jere, kuma su ne na daya a rukunin da suke neman tikitin shiga gasar kofin Turai.

Hodgson ya ce "Rooney yana taka rawar gani, amma ina jin tsoron nauyin da muka dora masa ya yi yawa, kuma kada ya shafi wasanninsa".

Rooney ya gaji mukamin kyaftin din Ingila ne a wajen Steven Gerrard, wanda ya yi ritaya daga buga wa kasar wasa, bayan da suka kasa taka rawar gani a gasar kofin duniya a Brazil.