Swansea ta zura wa Arsenal kwallaye 2-1

Swansea Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Swansea ta koma mataki na biyar a teburin Premier

Swansea ta samu nasara akan Arsenal da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata ranar Lahadi a filin wasa na Liberty.

Arsenal ta fara zura kwallo ta hannun Alexis Sanchez a minti na 63 kuma kwallo na 12 kenan da ya zura a gasar Premier a bana.

Swansea ta fara farke kwallon farko daga bugun tazara a yadi na 25, wanda Gylfi Sigurdsson ya buga ya kuma zura a ragar Arsenal.

Minti uku da farke kwallon farko dan wasan da ya shigo karawar Bafetimbi Gomis, wanda ya canji Wilfried Bony ya kara kwallo ta biyu a raga.

Nasarar da Swansea ta samu ya sa ta koma mataki na biyar a teburin da maki 18, yayin da Arsenal ke matsayi na shida da maki 17.