Newcatle ta lashe West Brom da ci 2-0

WestBrom vs Newcastle Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle ta dawo da tagomashinta a gasar Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta doke West Brom da ci 2-0 har gida a gasar Premier wasan mako na 11 da suka kara ranar Lahadi a The Hawthorns.

Newcastle ta fara zura kwallon farko ta hannaun Perez daf a tafi hutun rabin lokaci, kafin daga baya Coloccini ya kara ta biyu a minti na 62.

Nasarar da Newcastle ta samu ya sa ta koma mataki na 7 a gasar Premier da maki 16, bayan buga wasa na 11.

Bayan da Alan Pardew ya dawo da karsashin Newcastle, za su karbi bakuncin QPR a wasannin mako na 12, inda West Brom za ta ziyarci Chelsea a Stamford Bridge.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Sunderland 1 - 1 Everton

Tottenham 1 - 2 Stoke