Chelsea ce za ta lashe kofin Premier - Wenger

Arsenal Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta koma mataki na shida a kan teburin Premier

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce babu tantama Chelsea ce za ta lashe kofin Premier bana ganin yadda suke taka rawa a gasar.

Arsenal tasha kashi a hannun Swansea da ci 2-1 a karawar da suka yi ranar Lahadi, inda Chelsea ta ba ta tazarar maki 12.

Chelsea ta lashe wasanni tara daga cikin wasanni 11 da ta buga, kuma ta hada maki 29, ta bai wa Southampton tazarar maki hudu wacce ta ke mataki na biyu a teburin Premier.

Wenger ya ce "Idan har sunci gaba da kokari kamar yadda suke yi a yanzu, to babu wata kungiya da za ta iya tarar da su.

Kocin ya kara da cewa bai ji dadi ba a karawar da Swansea ta doke su, domin sune suka fara zura kwallo, kafin a farke a kuma kara musu.