Tarihin dan kwallon Gabon Pierre-Emerick Aubameyang

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aubameyang ya haskaka sosai a kakar wasan da ta wuce

Pierre-Emerick Aubamayeng ya sake shiga cikin 'yan wasan da BBC za ta zabi gwarzon dan kwallon Afirka karo na biyu a jere, hakan ya nuna irin rawar da yake taka wa a fagen tamaula, koda yake shi ne wanda bai buga gasar kofin duniya daga cikin 'yan wasa biyar da aka zabo ba.

Rashin halartar Gabon gasar kwallon kafa mafi girma a duniya, ya taimakawa dan wasanta cin moriyar kwallon kafa a tsawon lokuta.

A kakar bara, ya taimakawa Borussia Dortmund kai wa matsayi na biyu a gasar Bundesligar Jamus da kuma kofin FA da Bayern Munich ta lashe a jere, da kuma kai wa wasan daf da na kusa da karshe, wanda Real Madrid wacce ta lashe kofin ta fidda ita daga gasar.

Bayan da ya zura kwallaye 13 a gasar Bundesliga a bara, Aubameyang ya ci gaba da dora kwazonsa a kakar bana, inda ya zura kwallo a wasan farko da suka doke Bayern da ci 2-1 a gida.

Kamar yadda dan wasan ya fada, wannan ce gasar wasan da yafi fice, ganin yadda ya zura kwallaye uku daga cikin wasannin hudu da ya buga.

Haka kuma ana takaddamar cewar Aubamayeng mai shekaru ya kara samun kwarewar buga gasar zakarun Turai, musamma buga wasan gaba daga gefe ko kuma mai zura kwallo a raga.

A shekarar farko da ya fara bugawa Dortmund tamaula, ya ci zaman benci a manyan wasannin, amma da dama ta samu da Robert Lewandowski ya koma Bayern da kuma raunin da Marco Reus ya ji, sai Aubameyang ya amfana da damar da ya samu.

Bayan da ya zura kwallo daya tilo daga cikin wasannin tara a kakar farko da ya fara taka leda a Jamus, nan danan ya fara rufe bakin 'yan adawa, inda ya zura kwallaye uku na gani na fada daga wasanni hudu da ya buga wa Dortmund a bana.

Dan kwallon da aka haifa a Faransa amma ya zabi ya buga wa kasar mahaifinsa Gabon tamaula ya ce ya samu ci gaba da kuma karin kwarewa ne a Dortmund ganin yadda yanzu yake in yaren Jamus.

Ya fada a wata kafar yada labarai cewa a baya bana iya yin abinda koci Jurgen Klopp ya bukaci na yi, saboda bana jin yaren Jamus, saboda na tsibci kaina a wata sabuwar duniyar.

Tsohon dan kwallon Saint Etienne bayan da ya samu natsuwa lokacin da ya koma Dortmund a watan Yulin 2013 kan kudi fam miliyan 13, ya samu gurbin buga wa kulob din gasar kofin zakarun Turai a shekarar.

Aubameyang ya fara taka leda a matashin dan kwallo a AC Milan ta Italiya, kuma hakika sun yi rashin dan wasa mai kishirwar zura kwallo a raga.

Haka kuma dan wasan ya ci gaba da saka kaimi a tawagar 'yan kwallon Gabon a kokarin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, inda ya zura kwallaye biyu, ciki har da wasa mai mahimmaci da suka doke Burkina Faso a watan Oktoba.