Tarihin dan Nigeria Vincent Enyeama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Da kyar Messi ya zura kwallo a ragar Enyeama a Brazil

Tun lokacin da aka yi ikirarin Enyeama yana daya daga cikin masu tsaron raga da ya yi fice a nahiyar Afirka, ana kuma hasashen daya ne daga cikin wanda tauraruwarsa ke haskawa a Turai.

Kokarin da golan ya yi a kungiyar Lille a kakar bara, kimarsa ta kara fitowa da hakan ya sa ya kara martaba kansa a tarihi.

Dan kwallo Nigeria mai shekaru 32, wasanni karo 11 ya hana kwallo shiga ragarsa a gasar Faransa wato Ligue 1 a farkon kakar bara kafin a tafi hutu.

Jumulla, golan ya buge fenariti 21 a bara - babu wani mai tsaron raga a manyan gasar kasashe biyar din Turai da ya yi hakan.

Ya kuma kara samun martaba da a watan Mayu ya lashe kyautar mai tsaron baya da ya fi fice a gasar Faransa ta dan wasan Afirka da yafi hazaka a gasar.

Hakan ya kara masa azama da ya wakilci Nigeria a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, inda ya hana kwallaye da dama shiga ragarsa - har ma aka zabe shi mai tsaron raga na hudu da suka taka rawar gani a gasar.

Golan ya ci gaba da haskaka wa a raga, yayin da ya fara gasar bana da kafar dama a gasar Faransa da kuma nahiyar Turai.

Koda yake an dade ana hangen rashin kwarewar Enyeama - duk dakofunan da ya lashe a baya.

Ya dauki kofunan gasar zakarun Afirka karo biyu a 2003 da 2004 tare da kulob din Enyimba ta Nigeria, da kofin gasar Israeli da kofuna biyu da ya lashe a kulob din Hapoel Tel Aviv.

Enyeama ya kuma kara kaimi da ya bashi damar zura kwallaye 23 a raga a gasar Israeli ta bugun fenariti da bugun tazara.

Ficen da golan ya yi a kulob da Hapoel ya sa kungiyoyin Turai suka yi zawarcinsa da suka hada da Spaniya da Portugal da Turkiya da Rasha da Ukraine a kakar 2011, inda ya zabi ya buga wa Lille ta Faransa tamaula.

Hakan bai sa ya shiga kungiyar da kafar dama ba, dalilin da yasa ya koma Israel taka leda a watan Agustan 2012, inda ya koma kulob din Maccabi Tel Aviv abokiyar hamayyar Hapoel aro.

Hakan ya jawo masa bakin jini matuka, musamman daga magoya bayan Hapoel, inda suka dunga cin zarafin iyalansa, saboda fitatcen dan wasansu ya koma buga tamaula da abokiyar hamayyarsu.

Halin da ya shiga a lokacin yasa Enyeama ya kasa tabuka yin abin aza a gani tare da kulob din Maccabi.

Golan ya karawa kansa Martaba, inda ya lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013 da Afirka ta kudu ta karbi bakunci, kuma shi ne golan da ya fi fice a gasar.

Daga nan kuma nasarori suka dunga biyo baya, inda ya taimakawa Maccabi lashe kofuna biyu a gasar Israel karo biyu a 2013.

Enyeama ya sake haskakawa a gasar cin kofin nahiyoyi da aka buga a Brazil, inda ya hana kwallaye da dama shiga ragarsa, kuma hakan ne ma yasa Lille ta gayyato shi ya koma buga mata wasa.

Komawarsa Lille ta Faransa ya zo akan gaba, domin tuni ya samu kwarewa da gogewa a sana'arsa da hakan yasa nan danan ya haye kan ganiyarsa.

Enyeama dan wasan Nigeria ne na farko da ya fara lashe kyautar Marc-Vivien Foe a Faransa, kuma zai iya zama mai tsaron raga na farko a kasar da zai lashe gasar.