Tarihin dan kwallon Ivory Coast Gervinho

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gervinho ya sha suka lokacin yana taka leda a Arsenal

Tun lokacin da Gervinho ya koma Serie A daga gasar Premier dan wasan ya koma tagomashinsa, kuma ya na daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon Afirka.

A kakar wasan farko a kulob din Roma, dan kwallon mai shekaru 27, ya zura kwallaye 12 daga cikin wasanni 37 da ya buga, ya kuma zamo wanda yafi yawan bada kwallo a ci ga abokan wasansa da suka hada da Francesco Totti da kuma Torino Alessio wanda yanzu ya koma buga tamaula da Atletico Madrid.

Hakan yasa Roma ta samu tikitin buga gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko, wanda rabonta da haka tsawon shekaru hudu baya.

Bayan da suka dawo buga gasar zakarun Turan a watan Satumba, Gervinho ya zura kwallaye biyu a raga, kuma shi ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi taka rawa a karawar da suka doke CSKA Moscow 5-1.

Hakika kocin Roma Rudi Garcia yana cin moriyar kwarewa da kwazon dan kwallon Ivory Coast.

Gervinho, ya fara yin fice ne karkasnin Garcia a kulob din Lille ta Faransa, bayan da dan wasan ya fito da kansa a wasannin da ya buga wa Beveren and Le Mans.

A wasannin shekaru biyu kuma kakar karshe da ya buga wa kulob din Fransan, sun lashe kofin Faransa da kuma na gasar kasar, wanda rabonsu da kofin shekaru 56.

Gervinho, ya zura kwallaye 15 daga cikin wasannin 35 da ya buga, wanda hakan ne ma yasa manyan kungiyoyin Turai suka yi zawarcinsa.

Arsenal ce daga karshe ta samu daukar dan wasan, koda yake ya nuna zai iya taka rawar gani a kulob din, amma ya kasa nuna kwarewarsa.

Dan wasan ya kammala wasanninsa a Premier a 2013, lokacin da Garcia ya zamo kocin Roma ya kuma dauke dan kwallon.

Kamar yadda fitattun 'yan wasan Ivory Coast suka fara taka leda tun suna yara kamar su 'yan tagwaye Toure da Solomon Kalou, shi ma ya fara buga tamaula daga makarantar renon 'yan wasa ta ASEC academy dake Abidjan.

A makarantar ne Gervais Yao Kouassi abokan wasansa suka rada masa lakanin sunan kocin Brazil Gervinho.

Sunan kuma ya bishi a inda ya zamo dan kwallon Ivory Coast da yafi fice a gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil.

Gasar kofin duniya da suka buga bai yiwa kasar dadi ba, amma Gervinho ya samu yabo mai yawa a yadda ya taka leda a gasar.

Dan wasan ya zura kwallaye biyu, ciki har da wadda ya ci Colombia da kuma wadda ya bai wa Wilfried Bony da ya farke musu kwallon da Girka ta zura musu a wasannin cikin rukuni.

In banda Girogios Samaras ya kara cin Ivory Coast daf a tashi wasa, da kwallon da Bony ya farke ta kai kasar wasan zagayen gaba a gasar kofin duniya.

A cikin 'yan wasa da suka hada da Bony da Yaya Toure, Gervinho yana daga cikin fitattun 'yan kwallon Ivory Coast da ya zura kwallo a wasan farko da koci Herve Renard ya jagoranci tawagar kasar doke Saliyo 2-1.