Tarihin dan kwallon Ivory Coast Yaya Toure

Image caption Toure ne ya lashe kyautar a shekara ta 2013

A karo na biyar da ake saka sunan Yaya Toure cikin 'yan takarar kyautar dan wasan da yafi kwazo a Afirka, dan kwallon Ivory Coast sai a 2013 ya lashe kyautar.

Kuma kyauta ce da ta dace da dan kwallon da aka yi ittifakin ya yi fice cikin sa'o'insa da suke taka leda a zamanin.

A lokacin ne ya sanar wa da BBC cewa "lashe kyautar da ya yi abune mai cike da mamaki" inda ya bayya hakan da samun wani abu mashawuri.

Mai shekaru 31, ya yi kaurin suna wajen lashe kautuka a sanarsa na taka leda, wanda yake rungumar kalubale da hakan ya kara masa daraja a kulob dinsa da kasarsa tsawon shekaru da dama.

Zakakurin dan wasa da yake mamayar abokin hamayya da karfi da kuma buri, yana kuma jan kwallo har cikin da'ira ta 18, wanda hakan yasa yake yawan zura kwallaye a raga.

A bara ya yi barazanar zai bar Manchester City, saboda da dalilan mahukuntan kulob din sunki taya shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi.

Duk da fushin da ya yi da mahukuntan bai hana shi bada gudunmawa ga kulob din ba, inda suka lashe kofin Premier.

Haka kuma ya taimakawa City Lashe kofin Capital One Cup.

Kofuna biyu da Toure ya lashe da kuma kwallaye 20 da ya zura a raga, ya nuna cewar duk da bacin rai da ya shiga, bai hana shi taka rawa ba da kuma nuna kansa ba.

Sannan ya karawa kansa kima a City da iya cin kwallo a bugun tazara, musamman a mahimman wasanni, wanda hakan yasa ya zamo fitatcen dan kwallon kulob din.

Mutuwar kaninsa lokacin da ake gasar cin kofin duniya a 2014, ya kawo masa tsaiko a wasannin da ya buga wa Ivory Coast.

Rashin dan uwansa da ya yi ya shafi harkar wasansa, har ma ya kasa kokari a farkon kakar bana, a inda ya dunga shan suka na kasa taka rawar ganai a wasanninsa kamar yadda ya saba.

Sai dai ya samu karfin gwiwa daga City kamar yadda ya kamata, ganin yadda yake saka kwazo a kulob din tun lokacin da ya koma a 2010, ya kuma zamo daya daga cikin 'yan kwallon dake canja salon wasa kulob din ta yadda yake so.

A kasarsa ta Ivory Coast dan wasan na mutukar kokarin ganin ya taimakawa tawagar 'yan kwallon samun tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi.

Watakila wannan ce gasar karshe da dan kwallon zai so ya lashe kyauta ga Kasarsa da kansa, domin karfafawa 'yan baya gwiwa.

Rashin lashe kyautuka da Ivory Coast na daya daga cikin abinda Toure ya rasa a sana'arsa ta kwallon kafa, daga cikin kyaututtukan da ya lashe.

A cikin kyaututtukan da ya lashe akwai kofin La Liga Spaniya da kofunan Premier biyu da kofin zakarun Turai da Uefa Super Cup da kuma kofin duniya na zakarun kungiyoyin nahiyoyi.

Wannan ne karo na shida da aka saka sunansa a cikin 'yan wasan da za su iya lashe kyautar BBC ta gwarzon dan kwallon Afirka, kuma dan Afirka tilo dake cikin 'yan wasa 23 da ake sa ran fidda gwarzon dan kwallon kafar duniya na bana.