Sansanin Super Eagles ya tumbatsa da 'yan wasa

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigeria tana matsayi na uku a rukuni da maki hudu

Sansanin tawagar 'yan wasan kwallon kafar Nigeria ya cika makil da 'yan kwallon da ta gayyato domin karawa da Congo a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Kyaftin Vincent Enyeama da Ikechukwu Uche ne 'yan wasa na karshe da suka isa masaukin Super Eagles dake Bolton White a Abuja, Nigeria.

'Yan wasan biyu ba su samu halartar atisayenb da tawagar ta yi da yammacin Talata ba, wanda koci Stephen Keshi ya jagoranta.

Atisayen da Super Eagles ta yi da yammacin Talata a katafaren filin wasa na kasa dake Abuja ya kunshi jiga - jigan 'yan wasanta da ta gayyato domin buga mata wasa.

Keshi ya yi farin ciki da yadda 'yan wasan ke kan ganiyarsu, inda ya yi fatan za su dora har zuwa buga sauran wasannin da ya rage musu.

Nigeria wadda ta sha kashi a gida a hannun Congo da ci 3-1, za ta bakunci Congo a karawa ta biyu a Point Noire ranar Asabar.