Sturridge ya koma atisaye da Liverpool

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Daniel Sturridge na fatan komawa kan ganiyarsa a taka leda

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge ya koma atisaye da kulob din a karon farko tun lokacin da ya ji rauni a karawar da ya buga wa Ingila a cikin watan Agusta.

Liverpool ta lashe wasanni hudu daga cikin 14 da ta buga ba tare da Sturridge ya buga mata wasannin ba, sakamakon jinya da ya yi.

Sturridge. Mai shekaru 21, wanda ya zura kwallaye 21 daga cikin wasanni 29 a gasar bara, an sa ran zai dawo buga tamaula a makon jiya, amma hakan ya gagara.

Kocin Liverpool yana fatan dan wasan zai buga wasan da za su kara da Crystal Palace a gasar Premier wasan mako na 12 ranar 23 ga watan Nuwamba.

Liverpool tana mataki na 11 a teburin Premier, inda Chelsea wadda take matsayi na daya ta bata tazarar maki 15.