Carrick ba zai buga karawa da Slovenia ba

Micheal Carrick Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yasa ran zai buga wa Ingila wasa a makwonnan

Dan kwallon Ingila mai wasan tsakiya Michael Carrick, ba zai buga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za su kara da Slovenia, sakamakon rauni da ya ji.

Carrick, wanda rabon da ya buga wa Ingila wasa tun karawar da suka yi da Poland a bara, ya ji rauni ne a lokacin da yake atisaye da tawagar 'yan wasa.

Wani mai magana da yawun hukumar kwallon Ingila ya ce Carrick, zai koma sansanin kulob dinsa Manchester United, kuma ba zai buga wa Ingila wasa ba.

Haka kuma dan wasan ba zai buga wasan sada zumunta da Ingila za ta kara da Scotland ba.