World Cup 2022: Za a wanke Qatar kan cin hanci

World Cup 2022 Qatar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana takaddamar lokacin da za a fara wasannin cin kofin duniya a Qatar

Za a wanke kasar Qatar daga zargin bada cin hanci domin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2022, idan hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta fitar da rahotanta ranar Alhamis.

Tun a baya ana zargi mahukuntan kasar Qatar da bayar da cin hancin fam miliyan 3, domin a ba ta izinin karbar bakuncin wasannin kofin duniya.

Wani jami'in FIFA mai zaman kansa mai kula da da'a Hans Joachim Eckert, ne ake sa ran zai wanke kasar a rahoton da za a bayyana.

FIFA ta bai wa Rasha karbar bakuncin gasar kofin duniya a shekarar 2018 da kuma Qatar a 2022, a shekarar 2010, bayan da kwamitin amintattu ya kada kuri'ar raba gardama.

Kwamitin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na Qatar ya karyata dukkan zargin da ake masa.