Rasha ba za ta iya biyan albashin Capello ba

Fabio Capello Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabio Capello ya ce ya fara gajiya da rashin biyansa albashi

Hukumar kwallon kafar Rasha, FUR, ta ce ba za ta iya biyan albashin kocin tawagar kwallon kafarta Fabio Capello fam miliyan bakwai ba.

Rabon da tsohon kocin Ingila ya karbi albashi tun a watan Yuni, kuma ya fada a farkon watan nan cewar an kusa kai shi bango fa.

Capello dan kasar Italiya shi ne kocin tawagar kasar ra Rasha da ya ke daukar albashi mafi tsoka a duniya, inda ya linka albashin kocin Ingila Roy Hodgson har sau biyu.

Kocin ya tsawaita kwantiraginsa da Rasha a watan Janairu, wadda za ta kare bayan da kasar ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018.