La Liga ce gasar da ta fi yin fice a duniya - Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Moyes ya ce kungiyoyin Premier sun yi zawarcinsa a baya

David Moyes ya bayyana gasar cin kofin La Ligar Spaniya, da cewa ita ce gasar da ta fi yin fice a duniya, Moyes, ya fadi hakan ne a lokacin da aka gabatar da shi a sabon kocin kulob din Real Sociedad.

Moyes, mai shekaru 51, wanda Manchester United ta sallama a watan Afrilu, ya ce ya karbi aikin a Spaniya ne, bayan da ya ki amsa tayin kungiyoyin gasar Premier.

Kocin ya ce "Gasar La Liga ce take da fitattun 'yan wasa da kuma zakakuran masu horar wa, don haka na amince na karbi aiki a Sociedad domin na nuna kaina".

Moyes, ya rattaba hannu a kwantiragi da Sociedad na tsawon shekara guda kuma zai jagoranci kungiyar a karawar da za ta yi da Deportivo a gasar La Liga ranar 22 ga watan Nuwamba.