Neville ya goyi bayan komawar Moyes Sociedad

Moyes Neville Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Neville ya ce Moyes zai dawo da tagomashinsa a Spaniya

Phil Neville ya goyi baya da tsohon kocin Manchester United, David Moyes, ya karbi aikin horar da Real Sociedad ta Spaniya.

Dan kasar Scotland, mai shekaru 51, wanda United ta sallama bayan watanni goma da ya yi a Old Trafford, ya rattaba hannu a kwantiragi da Sociedad na tsawon shekara guda.

Neville ya kwashe watanni tara yana aiki tare da Moyes, a matsayin dan wasa a kulob din Everton da kuma mataimakin koci tare da United.

Tshohon dan wasan United Neville ya ce "Ya koma kungiyar da take da burin ci gaba da samun nasarori a wasanni kusan irin na kulob din Everton, saboda haka Moyes zai iya kai su gaci".