Magoya bayan Newcastle na son a kori Pardew

Alan Pardew Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Newcastle ta dawo da tagomashinta a gasar Premier

Magoya bayan kulub din Newcastle wadanda suke kamfe din a kori Alan Pardew sun ce har yanzu suna kan bakansu, kana sun yi watsi da nasarorin da kulob din ke samu a yanzu.

Doke West Brom 2-0 DA Newcastle ta yi ranar Lahadi, ita ce nasara ta biyar da kulob din ya yi a wasanni a jere, kuma kulob din ya koma matsayi na takwas a teburin Premier.

A kakar gasar Premier bara Newcastle wasanni biyar kacal ta lashe.

Masu son a kori kocin, wadanda suka bude shafin intanet sackpardew.com sun ce "Nasoririn da kulob din ke samu a yanzu ba zai sauya kiraye -kirayensu ba".

Pardew ya koma Newcastle a shekarar 2010, ya kuma tsawaita kwantiraginsa zuwa shekaru takwas a 2012, bayan da suka kare a mataki na biyar a gasar Premier.