Inter Milan ta kori kocinta Mazzari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Walter Mazzarri

Inter Milan ta kori kocin 'yan kwallonta Walter Mazzari sakamakon rashin rawar gani da kungiyar ke yi a gasar Serie A.

A watan Mayun 2013 ne aka nada Mazzari mai shekaru 53 domin jan ragamar kungiyar na tsawon shekaru biyu.

A kakar wasa ta bana, Inter Milan ta samu nasara a wasanni hudu cikin wasanni 11.

Tsohon kocin Manchester City, Roberto Mancini na daga cikin wadanda ake alankatawa da komawa Inter Milan din.

Wasan Inter na gaba shi ne da AC Milan a ranar 23 ga watan Nuwamba.