Ghana na daf da bayyana daukar Avram Grant

Avram Grant Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Avram Grant zai fuskanci kalubale daga kasashe da dama idan suka zo yin wasa

Hukumar kwallon kafar Ghana GFA, na daf da cimma yarjejeniyar kwantiragi na daukar Avram Grant a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar.

Grant, mai shekaru 59, kuma tsohon kocin kulob din Chelsea yana tattaunawa da hukumar kwallon Ghana kan kunshin kwantiragin da za su rattaba hannu a kai nan gaba.

Sai dai akwai fargabar cewa kocin dan kasar Israela, zai sami matsalar shiga wasu kasashen Arewacin Afirka.

Grant mai rike da fasfo din Israeli ba wai kawai da kasashen Arewacin Afrika zai sami matsala wajen shiga kasar su ba, har da ma kasashen Larabawa.

Ghana ta barar da damarta na samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan da Uganda ta doke ta daya mai ban haushi a karawar da suka yi ranar Asabar a Kampala.

Sai a ranar Laraba ne za a tantance sauran kasashen da za su sami tikitin buga babbar gasar kwallon kafar Afirka da Equitorial Guinea za ta karbi bakunci a badi.