Klitschko ya kare kambunsa a damben boxing

Wladimir Klitschko Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Karo na 17 kenan yana kare kambunsa na Damben boxing

Zakaran damben boxing ajin IBF da WBA da kuma WBO Wladimir Klitschko ya kare kambunsa bayan da ya dambace Kubrat Pulev a turmi na biyar ranar Asabar.

Klitschko, mai shekaru 38, dan kasar Ukraine ya kare kambunsa karo na 17 a jere kenan, kuma sau biyu yana kai Pulev kasa a tumin farko da kuma sau daya a turmi na uku.

Zakaran damben boxing Klitscko ya lashe wasan ne a turmi na biyar, kuma nasara ta 63 da ya samu, 53 a dukan kwaf daya, aka doke shi wasanni uku.

Dambace Pulev dan kasar Bulgaria da aka yi shi ne karon farko daga cikin wasanni 21 yana dambatawa.