Pillars ta lashe kofin Nigeria karo 3 a jere

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Kano Pillars zakarun kofin Premier Nigeria karo uku a jere

Kano Pillars ta lashe kofin Nigeria Premier League karo na uku a jere duk da doke ta 3-1 da Enyimba ta yi a karawar karshe na gasar bana da suka buga ranar Lahadi.

Tun a wasan mako na 37 Kano Pillars ta lashe kofin bana a lokacin da ta doke Nembe City da ci 4-0, kuma ta dauki kofuna a 2007-08 da 2011-12 da 2013 da kuma 2014.

Bayan kammala gasar bana Kano Pillars ta kare a matsayi na daya da maki 65, sai Enyimba a mataki na biyu da maki 64, sai Warri Wolves a mataki na uku da maki 61.

Tuni kungiyoyi hudu suka fado daga buga gasar Premier Nigeria da suka hada da Gombe United da Crown FC da Kaduna United da kuma Nembe City.

Kungiyoyin da za su maye gurbin su sun hada da Ranchers Bees da Wikki Tourist da 3 SC da kuma Gabros United.

Ga sakamakon wasannin mako na 38 da aka buga:

Crown FC 3 vs 0 Akwa United El-Kanemi Warriors 3 vs 0 Sunshine Stars Enyimba FC 3 vs 1 Kano Pillars Gombe United 4 vs 1 Abia Warriors Heartland 1 vs 2 Bayelsa United Kaduna United 1 vs 2 Enugu Rangers Lobi Stars 1 vs 0 Dolphin Nasarawa United 2 vs 2 Warri Wolves Nembe City FC 0 vs 4 Giwa FC Sharks 0 vs 1 Taraba FC