Nigerian Premier League: Wasannin karshe

NFF Logo
Image caption Wasannin mako na 38, na kuma karshen kakar bana

Za a buga wasannin karshe a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na 38 a filaye 10 dake fadin kasar.

Cikin wasannin da za a kara kungiyar Kano Pillars za ta fafata da Enyimba a garin Aba, sai kuma Kaduna United ta karbi bakuncin Enugu Rangers.

El-Kanemi za ta barje gumi da Sunshine a Kano, Nasarawa United ta karbi bakuncin Warri Wolves, sai wasan hamayya tsakanin Heartland da Bayelsa United.

Tuni dai Kano Pillars ta lashe kofin bana da maki 65, inda Enyimba ke mataki na biyu da 61, sai Warri Wolves a matsayi na uku da maki 60.

Kungiyoyi hudu ne ake sa ran za su yi sallama da gasar Premier bana, wanda tuni aka samu Kaduna United da Crown Fc da kuma Nembe City suka fado daga gasar.

Ga wasannin mako na 38 da za a buga a filaye daban-daban:

Crown FC vs Akwa United El-Kanemi Warriors vs Sunshine Stars Enyimba FC vs Kano Pillars Gombe United vs Abia Warriors Heartland vs Bayelsa United Kaduna United vs Enugu Rangers Lobi Stars vs Dolphin Nasarawa United vs Warri Wolves Nembe City FC vs Giwa FC Sharks vs Taraba FC