Dan wasan United Daley Blind ya ji rauni

Daley Blind Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blind shi ne dan wasan United na uku da ya ji rauni a karshen mako

Dan kwallon Manchester United Daley Blind ya ji rauni a lokacin da ya ke buga wa kasarsa Netherlands wasa a karshen mako.

Dan wasan, mai shekaru 24, ya fadi a fili dai-dai minti na 20 da fara karawar da suka doke Latvia 6-0, a gasar neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Blind wasanni takwas kacal ya buga wa United tun lokacin da ya koma buga wa kulob din wasa a bana daga, Ajax kan, kudi sama da fam miliyan 13.

Dan wasan shi ne dan kwallon United na uku da ya ji rauni a lokacin da suke buga wa kasashen su wasanni da suka hada da David De Gea da kuma Michael Carrick.