Nigeria na harin tikitin shiga gasar kofin Afirka

Nigeria Soth Afirca Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ce a mataki na biyu da maki 7, sai Congo a matsayi na uku da maki 7 a rukuni na daya

Tawagar Super Eagles mai rike da kofin Nahiyar Afirka na fatan samun tikitin shiga gasar badi, a karawar da za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu ranar Laraba.

Nigeria ta sami karfin gwiwa ne bayan da ta doke Congo da ci 2-0 a ranar Asabar da ya wuce, kuma hakan yasa Super Eagles ta koma mataki na biyu a rukunin da maki bakwai.

Afirka ta Kudu ce ke matsayi na daya a rukunin da maki 11, kuma tuni ta samu gurbin buga wasannin badi, bayan da ta sami nasara a kan Sudan da ci 2-1 ranar Asabar

Tuni kasashe tara suka samu tikitin shiga gasar badi, sauran gurbin kasashe shida ya rage, wadda Equitorial Guinea mai masaukin baki ta maye gurbin Morocco.

Za a fara fafatawa a gasar wasan kwallon kafa mafi girma a Nahiyar Afirka kamar yadda CAF ta tsara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Ga wasannin da za a buga ranar Laraba:

Iv Coast v Cameroon DR Congo v S Leone Ethiopia v Malawi Mali v Algeria Ghana v Togo Guinea v Uganda Niger v Mozambique Zambia v Cape Verde Nigeria v South Africa Sudan v Congo Burkina Faso v Angola Gabon v Lesotho Senegal v Botswana Tunisia v Egypt