Manchester United ta yi hasarar kudin shiga

Old Trafford Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption United ta samu faduwar ne sakamakon kasa samun tikitin shiga gasar zakarun Turai

Kungiyar Manchester United tace kudaden shigar da take samu sun ragu da kusan kashi 10 cikin dari, a watanni uku na rubu'i na uku na wannan shekarar.

Kungiyar tace kudin shigar sun fado ne zuwa fam miliyan 88.7 a karshen watan Satumba.

United ta yi rashin samun kadin shigar ne sakamakon kasa samun tikitin shiga gasar zakarun Turai a bara, dalilin da ya sa Nike yaki bai wa United kudin dawainiya.

Shugaban kungiyar Ed Woodward ya ce kasuwancin United a shekarar 2014-15, zai samu tsaiko ne saboda kasa samun gurbin buga gasar cin kofin zakarun Turai da ba su yi ba.

United ta rattaba hannu a kwantiragin fam miliyan 750 tare da kamfanin Adidas da za ta fara aiki a farkon kakar badi.