AFCON 2015: Ivory Coast ta sami tikitin gasar

Ivory Coast Cameroon Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ivory Coast ta sami tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka

Ivory Coast ta sami tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, da Equitorial Guinea za ta karbi bakunci, bayan da suka tashi wasa babu ci da Kamaru.

Tuni dai Kamaru ta sami gurbin buga gasar kofin nahiyar Afirka kafin su kara a Abidjan, kuma ta karasa fafatawar ne da 'yan wasa 10, bayan da aka bai wa Stephane Mbia jan kati.

An kori kyaftin din Kamaru Stephane Mbia ne, bayan da ya yiwa dan kwallon Ivory Coast Gervinho keta daf da da'ira 18 ta Kamaru.

Daya karawar ta cikin rukunin Jamhuriyar Congo ta doke Saliyo da ci 3-1.