Ballon d'Or 2014: 'Ya kamata dan Jamus ya lashe'

Germany Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus ne suka lashe kofin duniya da aka kammala a Brazil

Louis van Gaal ya ce ya kamata dan kwallon Jamus ya lashe kyautar dan wasan da yafi yin fice a duniya a bana, saboda lashe kofin duniya da suka yi a Brazil.

Ana hasashen tsakanin Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ne za su kasance kan gaba sai kuma dan wasan United Angel Di Maria, wajen lashe kyautar gwarzon kwallon kafa na bana.

Van Gaal ya ce 'yan wasan Jamus sun taka rawa a gasar kofin duniya da aka kammala, sannan gasar Bundesliga tana kara yin fice a duniya.

Kocin ya kuma ce ya yi mamaki da aka saka sunan shi a cikin 'yan takarar da za a fitar da gwarzon mai horar da kwallon kafa na shekarar nan.