Sturridge zai sake jinyar makonni shidda

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sturridge ya sami koma baya a gasar wasannin baya sakamakon jinya

Dan kwallon Liverpool, Daniel Sturridge zai sake sabuwar jinya ta makwonni shidda, sakamakon raunin da ya kara ji.

Sturridge ya ji rauni ne a cinyarsa ranar Talata, kuma likitoci sun duba shi, inda suka gano wani raunin da ya bambanta da wanda dan wasan ya ji.

Dan kwallon, mai shekaru 25, ya dawo atisaye ne a makon jiya bayan jinyar rauni da ya yi, kuma wasanni uku ya buga a gasar Premier bana.

Dan wasan ya ji rauni ne a watan Satumba lokacin da yake buga wa tawagar Ingila wasa, ya kara samun rauni na biyu a watan Oktoba, a lokacin da suke atisaye.

Liverpool ta lashe wasanni hudu daga cikin karawa 14 a wasannin da ta buga, ba tare da Sturridge ba, kuma tana matsayi na 11 a teburin Premier.