Sturridge na Liverpool ya kara jin rauni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool na cikin matsala saboda rashin Sturridge

Dan kwallon Liverpool, Daniel Sturridge ya kara jin sabon rauni a lokacin horo a ranar Talata.

Dan shekaru 25, ya ji rauni a cinyarsa kuma a ranar Laraba za a dauki hoton kafarsa domin sannin tsananin raunin.

Sturridge wanda ya zura kwallaye 25 a kakar wasan da ta wuce ya buga wasanni uku ne kacal a kakar wasan da muke ciki.

Tun a watan Satumba ya ji rauni lokacin yana horo tare da Ingila sannan kuma ya kara jin ciwo a watan Oktoba.

A yanzu haka Liverpool na tsaka mai wuya inda ta samu nasara a wasanni hudu cikin 14 da ta buga.