Federer ya sami sauki, zai buga Davis Cup

Roger Federer Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Federer a wasan karshe ciwon baya ya hana shi karawa da Djokovic

Roger Federer ya sami sauki daga raunin da ya ji a bayansa, kuma zai buga gasar kwallon Tennis ta Devis Cup da za a fara ranar Juma'a.

Federer zai buga wasa na biyu ne ranar Juma'a, inda zai fafata da Gael Monfils a karawa tsakanin Switzerland da Faransa da za su barje gumi a Lille.

A makon jiya ne Federer ya janye daga buga wasan karshe da ya kamata ya buga da Novak Djokovic sakamakon ciwon baya.

Federer zai wakilci Switzerland tare da Stan Wawrinka duk da takardamar da ta barke tsakaninsa a lokacin gasar da aka kammala a Landan