Manchester United ta doke Arsenal 2-1 har gida

Arsenal Manunited Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United ta koma matsayi na 4 a teburin Premier, Arsenal ta koma mataki na 7

Kulob din Arsenal ya yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka buga a filin Emirates ranar Asabar.

United ta fara zura kwallon farko a inda Gibbs ya ci gida a kwallon da Valenciya ya buga a minti na 56, kafin Rooney ya kara kwallo ta biyu a minti na 85.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun dan wasanta Olivier Giroud daf a tashi daga wasa.

Nasarar da United ta samu yasa ta koma mataki na hudu da maki 19 a teburin Premier, inda Arsenal ta koma matsayi na bakwai da maki 17.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Chelsea 2 - 0 West Brom Everton 2 - 1 West Ham Leicester 0 - 0 Sunderland Man City 2 - 1 Swansea Newcastle 1 - 0 QPR Stoke 1 - 2 Burnley