Tottenham ta doke Hull da ci 2-1 har gida

Hull Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham ta koma matsayi na 10 a teburin Premier da maki 17

Tottenham ta doke Hull City da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka kara a filin wasa na KC Stadium ranar Lahadi.

Hull City ce ta fara zura kwallon farko ta hannun dan wasanta Jake Livermore daga yadi na 25, lokacin da Hatem Ben Arfa ya yi kokarin zura kwallon a raga.

Tottenham ta farke kwallo ta hannun Harry Kane ta kuma kara ta biyu ta hannun Christian Eriksen daf a tashi daga wasan.

Hull ta kammala wasan da 'yan wasa 10 a fili, inda aka bai wa Gaston Ramirez jan kati, saboda ketar da ya yiwa Jan Vertonghen.