Mourinho ya yi murna da kokarin Chelsea

Jose Mourinho
Image caption Chelsea ta buga wasanni 12 a gasar Premier har yanzu ba a doke ta ba

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce wasan da suka doke West Bromwich Albion 2-0 a gasar Premier, shi ne wasan da kulob din ya buga da tafi burge shi tun zamowarsa kocin Chelsea.

Chelsea wadda ke mataki na daya a teburin Premier, ta kuma bayar da tazarar maki bakwai, bayan da Diego Costa da Eden Hazard suka zura kwallaye biyun da suka doke West Brom.

Mourinho ya taba horar da Chelsea a shekarar 2004 zuwa 2007, yanzu ya kwashe watanni 18 a matsayin kocin kulob din karo na biyu.

Doke West Brom da Chelsea ta yi ranar Asabar ya sa ta kafa tarihi a kulob din, inda ta buga wasanni 12 ba tare da an doke ta ba a farkon kakar wasan bana.