Messi ya kafa tarihin yawan zura kwallaye

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ya zura wa kulob din Barcelona kwallaye 368 a raga

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce ba za a sami dan wasan da zai karya tarihin da Lionel Messi ya kafa na dan wasan da yafi zura kwallo a raga a gasar La-Liga Spaniya ba.

Barcelona ta doke Sevilla da ci 5-1 a gasar La-Liga wasan mako na 12 da suka buga ranar Asabar, kuma Messi ne ya zura kwallaye uku a raga a karawar.

Messi, mai shekaru 27 ya zura kwallaye 253 a raga kenan jumulla, inda ya karya tarihin da Telmo Zarra ya kafa wanda ya zura kwallaye 251 tun a shekarar 1955.

Enrique ya ce zai yi wuya a karya tarihin da Messi ya kafa, tunda har yanzu yana buga gasar kuma zai ci gaba da zazzaga kwallaye a raga.

Sai dai kuma wani dan wasan da shima yake zura kwallaye a gasar La-Liga shi ne Cristiano Ronaldo, mai shekaru 29 dan wasan Real Madrid, inda ya zura kwallaye 197 a raga.