An rufe zaben gwarzon kwallon Afirka na BBC

AFOY 2014
Image caption Ranar Litinin 1 ga watan Disamba za a sanar da zakaran bana

An rufe zaben gwarzon dan kwallon kafar Afirka na shekarar 2014 da BBC za ta karrama a bana ranar Litinin 24 ga watan Nuwamba da karfe 06:00 na yamma agogon GMT.

Za a sanar da wanda ya lashe kyautar bana ne ranar Litinin, 1 ga watan Disamba, a lokacin da ake gabatar da shirin BBC na Focus on Africa a Talabijin.

Cikin 'yan takara hudu daga cikin wadanda aka zabo a bana sun buga gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, wanda a karon farko kasashe biyu daga Afrika suka kai matakin wasan zagaye na biyu.

Mai tsaron raga Enyeama dan kwallon Nigeria ya kai matakin wasan kasashe 16 da suka rage a gasar da kuma Brahimi dan wasan Algeria.

Enyeama, mai shekaru 32, ya buga gasar ne da kwazon da ya samo a gasar Faransa da kungiyar Lille inda wasanni 21 ya hana kwallo ta shiga ragarsa.

A Spaniya, kwazon da Brahimi ya saka a Granada ya sa aka zabe shi dan kwallon Afirka da ya fi fice a kasar a bara, inda ya bashi damar komawa Porto buga tamaula.

Yan wasan sun nuna bajintar da yasa suka haskaka a wasanninsu- haka shi ma dan wasan Roma Gervinho, inda ya dawo da tagomashinsa a Italiya, bayan da ya bar Premier tare da Arsenal inda ya zura kwallaye 10 daga wasanni 39 da ya buga a Serie A.

Mai wasan tsakiya Yaya Toure ya mance da sabanin da suka samu da mahukuntan City, inda ya taimakawa kulob din lashe kofin Premier karo na biyu a cikin shekaru uku, ya kuma lashe kofin Capital One Cup.

Koda yake Aubameyang bai buga gasar kofin duniya ba saboda Gabon ba ta samu tikitin shiga gasar ba, amma ya samu shiga takarar kyautar da BBC ke bayarwa a karo na biyu a jere, bayan da ya saki jiki a kulob din Dortmund.

Dan kwallon mai shekaru 25 ya nuna kansa a gasar cin kofin zakarun Turai a bana inda ya riga ya zura kwallaye uku a raga.

Ga jerin 'yan wasan da suka lashe kyautar BBC ta gwarzon dan kwallon Afrika a baya:

2013 - Yaya Toure (Ivory Coast da Manchester City)

2012 - Chris Katongo (Zambia da Chinese Construction)

2011 - Andre 'Dede' Ayew (Marseille da Ghana)

2010 - Asamoah Gyan (Sunderland da Ghana)

2009 - Didier Drogba (Chelsea da Ivory Coast)

2008 - Mohamed Aboutrika (Al Ahly da Masar)

2007 - Emmanuel Adebayor (Arsenal da Togo)

2006 - Michael Essien (Chelsea da Ghana)

2005 - Mohamed Barakat (Al Ahly da Masar)

2004 - Jay Jay Okocha (Bolton da Nigeria)

2003 - Jay Jay Okocha (Bolton da Nigeria)

2002 - El Hadji Diouf (Liverpool da Senegal)

2001 - Sammy Kuffour (Bayern Munich da Ghana)

2000 - Patrick Mboma (Parma da Kamaru)