Casillas yana cikin zaben gwarzon gola

Iker Casillas

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Casillas yana cikin 'yan tararar wanda za a zaba a golan da yafi yin fice a bana

Golan Real Madrid dan kasar Spaniya Iker Casillas yana cikin sunayen masu tsaron raga da za a zabi gwarzon golan da yafi yin fice a bana.

Sauran masu tsaron raga da suke cikin 'yan takarar su ne golan Chelsea Thibaut Courtois da na Bayern Munich, Manuel Neuer da na Barcelona Claudio Bravo da kuma na Juventus Gianluigi Buffon.

Sai dai kuma saka sunan Casillas a cikin 'yan takara ya bada mamaki, duk da cewar golan ya kama wa Madrid wasa tsawon shekaru biyar daga 2008 zuwa 2012.

Wasanni biyu kacal Casillas ya buga a gasar La Liga 2013-14, sannan ya kama gola a wasanni 10 a kakar bana.

Casillas mai shekaru 33 da haihuwa, an dora masa alhakin doke Spaniya da aka yi a gasar cin kofin duniya musamman karawa da Netherlands da kuma Chile.

'Yan wasa 20,000 ne daga fadin duniya za su fidda gwarzon golan bana da za a bayyana wanda ya lashe kyautar ranar 12 ga watan Janairu lokacin kyautar Ballon d'Or.