Rodgers ya dauki alhakin rashin kokarin Liverpool

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Liverpool wadda ta kare a matsayi na 2 a bara, ta kasa taka rawar gani a bana

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya amince da daukar alhakin kasa tabuka rawar gani da Liverpool take fama da shi a kakar wasannin bana.

Liverpool wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier, ta yi rashin nasara a wasannin Premier uku a jere, kuma na shida a bana, bayan da Crystal Palace ta doke ta da ci 3-1.

Rodgers ya ce "Ya shiga tsaka mai wuya, kuma abin da yake bukata nemar wa kansa da kuma kulob din mafita".

Liverpool wadda ta lashe wasa daya daga cikin wasanni biyar a baya data buga, tana da tazarar maki 18 tsakaninta da Chelsea wadda take matsayi na daya a teburin Premier.

Ranar Laraba Liverpool za ta kara da Ludogorets Razgrad a Bulgaria a gasar cin kofin zakarun Turai.