'Ba zan dauki fansa kan Chelsea ba'

Di Mateo
Image caption Kocin ya taka rawar gani a lokacin da ya horar da Chelsea

Tsohon mai horar da 'yan wasan kulob din Chelsea Roberto Di Matteo ya ce ba daukar fansa ne ya sa a gaba ba a wasan da kulob dinsa na Schalke zai dauki bakuncin Chelsea a gasar Zakarun Turai.

Kulob din Chelsea ya sallami Di Matteo mai shekaru 44 ne watanni shida bayan ya ciwo wa Chelsea kofin gasar zakarun Turai a shekarar 2012.

Ya ce "Na kwashe shekaru masu yawa a Chelsea, amma yanzu ba lokaci ba ne na nuna son rai ba, Ni dai ina so na doke kulob din.

"A ranar Talata za mu mayar da hankali kan wasan, ba ni da wani tunani na ramuwar gayya." In ji Di Matteo.

Di Matteo ya buga wa Chelsea a wasanni 175 daga shekarar 1996 zuwa 2002, inda kulob din ya dauki kofuna biyu na gasar FA, kafin ya zama mai horar da 'yan wasan kulob din a shekaru biyun da suka wuce.