Wilshare zai gana da kwararren likitan kafa

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan yana fama da ciwon raunin kafa

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshere, zai gana da kwararren likitin kafa domin ya duba raunin da ya ji a karawar da suka yi da Manchester United a gasar Premier.

Dan wasan Ingila, mai shekaru 22, ya ji raunin ne lokacin da dan wasan United Paddy McNair ya yi masa keta bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wilshere ya yi kokarin karasa wasan da raunin da ya ji a kafarsa, amma sai sauya shi aka yi.

Arsenal za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba, ta kuma kara da West Brom a gasar Premier ranar Asabar.