Manchester City ta doke Bayern Munich 3-2

Sergio Aguero
Image caption Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3-2

Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3-2 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a filin wasa na Ettihad ranar Talata.

Sergio Aguero ne ya fara zura kwallon farko da bugun fenariti a minti na 21 da fara kwallo, bayan da Benatia ya yi masa keta aka kuma bashi jan kati.

Munich ta farke kwallonta ta hannun Alonso a minti na 40, kafin ta kara ta biyu ta hannun Lewandowsi daf da tafiya hutun rabin lokaci

Bayan da aka dawo wasa ne Sergio Aguero ya farke kwallon da Munich ta zura musu a minti na 85, kuma wasa ya koma 2-2, ya kuma kara ta uku daf da tashi wasa.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

CSKA 1 - 1 Roma Apoel Nic 0 - 4 Barcelona Paris St G 3 - 1 Ajax Schalke 0 - 5 Chelsea Sporting 2 - 1 NK Maribor BATE Bor 0 - 3 FC Porto Shakt Donsk 0 - 1 Ath Bilbao