U 17: Ghana za ta san matsayinta

Ghana u17
Image caption Ranar Laraba ne CAF za ta yanke hukunci idan Ghana za ta buga gasar badi a Niger

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, za ta yanke hukuncin da Ghana ta shigar kan korarta da hukumar ta yi daga gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 na badi.

CAF, ta hukunta kasar ne sakamakon samun ta da laifin yin amfani da dan wasa Isaac Twum, wanda shekarunsa suka wuce ka'ida a karawar da suka yi da Kamaru.

Ghana ce ta lashe wasan da suka buga ranar 13 ga watan Satumba da ci 2-1, jimillar haduwa biyu da suka yi ta zura kwallaye 6-4.

Daga baya Kamaru ta shigar da kara, kuma CAF ta samu Ghana da laifi ta kuma dakatar da ita daga shiga gasar wasannin da Niger za ta karbi bakunci a badi.