Arsenal ta kai wasan zagayen gaba a kofin Turai

Arsenal Borussia Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsenal na matsayi na biyu a teburi da maki 10

Kulob din Arsenal ya doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun Turai wasan karo na biyu da suka kara a filin wasa na Emirates ranar Laraba.

Arsenal ta fara zura kwallon farko ta hannun Yaya Sanogo a minti na biyu da fara taka leda, kafin Alexis Sanchez ya kara ta biyu a minti na 57.

A karawar farko da suka buga a Jamus, Borussia Dortmund ce ta doke Arsenal da ci 2-0.

Nasarar da Arsenal ta samu ta kai ta zagayen gaba na gasar cin kofin zakarun Turan da maki 10 a matsayi na biyu, inda Borussia ke a matsayi na daya da maki 12.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Atl Madrid 4 - 0 Olympiakos Malmö FF 0 - 2 Juventus FC Basel 0 - 1 Real Madrid Ludo Razgd 2 - 2 Liverpool Zenit St P 1 - 0 Benfica Bayer Levkn 0 - 1 Monaco Arsenal 2 - 0 Bor Dortmd Anderlecht 2 - 0 Galatasaray