Victor Moses zai yi jinya

Victor Moses
Image caption Victor Moses dan wasan Chelsea da Super Eagles

Dan kwallon Stoke City da ke buga mata wasa aro, Victor Moses zai yi jinya na tsawon sati takwas.

Moses, dan wasan Chelsea ya kwashe kakar bara a kulob din Liverpool aro, inda ya ci kwallo guda a wasanni 12 da ya buga wa Stoke City a gasar Premier.

Sai dai dan wasan Stoke Marc Wilson mai tsaron baya, wanda bai buga karawar da suka yi da Burnley ba, ya murmure daga jinyar da ya yi.

Stoke tana matsayi na 11 a teburin Premier, kuma za ta ziyarci Liverpool a Anfield ranar Asabar.