Hukumar FA na tuhumar Dave Whelan

Dave Whelan
Image caption Whelan ya nemi afuwa bisa jawabin da ya yi

Hukumar kwallon kafar Ingila na tuhumar shugaban kulob din Wigan Dave Whelan, bisa batun da ya yi a kan yahudawa da Sinawa a hirar da aka yi da shi.

Hukumar FA ta bashi zuwa 5 ga watan Disamba domin ya kare kansa. Whelan, mai shekaru 77, ya nemi gafara bisa batun da ya yi.

An zargi shugaban da yin kalamai da suka jibanci zagi da cin zarafi da rashin ladabi da zai iya kawo rikici a lokacin wasa.

Whelan ya tsaya kai da fata cewar ba a fahimci jawabin hirar da ya yi a jaridar bane.