FIFA na binciken Franz Beckenbauer

Franz Beckenbauer Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption FIFA na binciken manyan jami'anta kan zargin cin hanci

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA na binciken Franz Beckenbauer a kan rawar da ya taka kan zabar Russia da Qatar wajen karbar bakuncin cin kofin duniya.

Beckenbauer, mai shekaru 69, yana daga cikin mutane 22 da suka kada kuri'a a shekarar 2010 kan kasashen da za su karbi bakuncin gasar kofin duniya na 2018 da 2022.

Shi ma mai neman takarar kujerar shugabancin FIFA, Harold Mayne-Nicholls, wanda ya yi bincike kan kasashen da suka shiga takarar karbar bakunci, yana daga cikin wadanda ake bincika.

Jami'in FIFA mai kula da da'ar ma'aikata, Michael Garcia yana kuma binciken wasu manyan jami'an FIFA uku.

Manyan jami'an kwamitin amintattun FIFA da ake bincike sun hada da Angel Maria Villar Llona daga Spaniya da Michel D'Hooghe daga Belgium da kuma Worawi Makudi daga Thailand.