Wilshere zai yi jinyar watanni uku

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wilshere sai a cikin shekara mai zuwa zai dawo taka leda

Kulob din Arsenal ya sanar da cewar Jack Wilshere, zai yi jinya watanni uku, bayan da likitoci suka yi masa tiyata a kafarsa ta hagu.

Wilshere ya ji raunin ne a lokacin da suka kara a wasan da Manchester United ta doke su da ci 2-1 a gasar Premier ranar Asabar.

Dan wasan United, Paddy McNair ne ya yi wa dan kwallon Ingila, mai shekaru 22 keta, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Arsenal ta kai wasan gaba a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 ranar Laraba.

Ranar Asabar ne kuma Arsenal za ta ziyarci West Bromwich Albion a gasar Premier wasan mako na 13.