Angel Di Maria zai yi jinya

Angel Di Maria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana sa ran dan wasan zai murmure cikin gaggawa

Dan kwallon Manchester United Angel Di Maria, ba zai buga karawar da za suyi da Stoke City ranar Talata ba, sakamakon raunin da ya ji.

Dan wasan mai maisheru 26 ya ji rauni ne a karawar da United ta doke Hull City 3-0 a gasar Premier ranar Asabar.

Di Maria tsohon dan kwallon Real Madrid da United ta sayo kan kudi sama da fam miliyan 59, ya shiga cikin jerin 'yan wasan United da su ke fama da jinya.

'Yan wasan United da ke yin jinya sun hada da mai tsaron baya Jonny Evans, da Luke Shaw, da Phil Jones, da Rafeal da kuma Daley Blind.