Brahimi ya lashe kyautar gwarzon BBC na 2014

Image caption Brahimi ya ce kyautar zata kara karfafa mushi gwiwa

An sanar da Yacine Brahimi na kasar Algeriya a matsayin gwarzon dan kwallon Afrika na BBC na bana.

Masu sha'awar kwallon kafa daga kasashe 207 ne suka kada kuri'ar zaban Yacine Brahimi, daga cikin 'yan wasa da suka hada da Vincent Enyeama na Najeriya, da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon, da Gervinho da kuma Yaya Toure na Ivory Coast.

Brahimi ya ce ya yi farin ciki da zabansa da aka yi, sannan ya gode wa mutanen da suka zabe shi.

Ya ce kyautar zata kara karfafa mashi gwiwa, yadda zai cigaba da taka rawar gani.

A shekarar 2014, Yacine Brahimi ya taka rawar gani a fagen tamaula a kulob dinsa da kuma kasarsa.